Alqur'ani mai girma

Rubutun addinin musulunci na tsakiya

Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda akasani, shine littafin da Allah ya Saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani Littafi Mai tsarki a bayansa, (babu littafin da Allah zai sake saukarwa a bayansa) kamar yadda Allah ya saukar ga Annabawan da suka gabata, domin Annabi Muhammadu shine cika makin Annabawan Allah.

Alqur'ani mai girma
Asali
Shekarar ƙirƙira631
Asalin sunaالقرآن‎
haɗawa aMakkah da Madinah
Characteristics
Genre (en) Fassarareligious literature (en) Fassara da religious text (en) Fassara
HarsheIngantaccen larabci
Kintato
Narrative location (en) FassaraYankin Larabawa
masu karatun alqur'ani mai girma

Wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Annabi Muhammad (S A W). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin aƙidar Musulunci, Ƙur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammad (S.A.W), yana tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S A W) Manzone na gaskiya.[1]

Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Ƙur'ani (Madogararsa na Farko), shine littafin da Musulmai suke karantawa, kuma suke aiki dashi, tare da hadisai Waɗanda suke sune maganar da fito daga harshen Annabi Muhammad. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.

Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na ɗan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.[2]

Hotuna gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. dictionary.reference.com: koran
  2. https://www.iusinitinere.it/clash-between-sharia-law-and-human-rights-in-light-of-pace-resolution-2253-23827