Shawwal (Larabci شوال) shine watan goma cikin jerin watannin Musulunci na shekara.

Shawwal
calendar month (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare naHijri month (en) Fassara
MabiyiRamadan
Ta biyo bayaDhu al Ki'dah

Azumi a watan Shawwal gyara sashe

Ranar farko ta watan shawwal itace ranar Idin karamar sallah. An sunnanta ma musulmai yin azumi na kwana shida a watan Shawwal bayan kammala azumtar dukkannin watan Ramadan. Amma an haramta yin azumi a ranar Idi wato ranar farko ta watan shawwal ko ranar Sallah karama.

Lokuta gyara sashe

Lokuta a watan shawwal daga shekara ta 2016 zuwa 2021

Bayan hijiraRanar FarkoRanar Karshe
143706 Yuni 201603 Ogusta 2016
143826 Yuni 201723 Yuli 2017
143915 Yuni 201813 Yuli 2018
144004 Yuni 201903 Yuli 2019
144124 Mayu 202021 Yuni 2020
144213

Mayu 2021

10 Yuni 2021
Kwanakin watan shawwal tsakanin shakarar 2016 da 2021

Abubuwan tarihi gyara sashe

  • Ranar 01, Bikin karamar Sallah ko Eid al-Fitr
  • Ranar 08, Masarautar Saudiyya ta rusa makabartun Jannatul Baqee da Jannatul Mualla a 1926
  • Ranar 13, Haihuwar malamin Sunnah Muhammad Al-Bukhari An haifeshi a shekara ta 194 bayan hijira
  • Ranar 22, rasuwar Haji Dost Muhammad Qandhaji, babban malamin Sufanci dan kasar Afganistan
  • Ranar 24, Rasuwar Ghulam Farid Sabri da Makbool Ahmed Sabri
  • Ranar 25, Shahadar Imam Ja'afar Assadik